1 Agusta 2016 - 10:50
Ayat. Khamenei: Yarjejeniyar Nukiliya Ya Tabbatar Da Cewa Amurka Ba Abar Yarda Ba Ce

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar yarjejeniyar nukiliya da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya ya tabbatar da cewar babu amfani wata tattaunawa da Amurka da kuma cewa ita ba abar yarda ba ce.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a yau din nan Litinin da dubun dubatan mutanen da suka fito daga jihohi daban-daban na Iran inda ya ce yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma ya tabbatar rashin amfanin tattaunawa da kulla yarjejeniyar da Amurka, da kuma cewa lalle ita ba abar yarda ba ce, kamar yadda kuma ya tabbatar da cewa hanya guda kawai ta tabbatar da ci gaban kasa ita ce dogaro da kai da kuma irin karfin da ake da shi a cikin gida, ba wai makiyan da a kullum ba abin da suka sa a gaba in banda kafar ungulu da duk wani kokari na ci gaban kasar ba.

Yayin da kuma yake magana kan kokarin da kasar Saudiyya ta ke yi na kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila, Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan a matsayin babban ha'inci kana kuma cin kafar al'ummar musulmi, daga nan kuma sai ya ce: Ko shakka babu wannan kulla alakar babban kuskure da kuma cin amana ne.

Haka nan kuma yayin da ya koma kan abin da ke faruwa a kasar Bahrain kuwa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce amfani da karfin soji da wasu kasashen waje suke yi a kan al'ummar Bahrain wani kokari ne na rufe bakin al'ummar kasar da kuma tilasta musu abin da ba sa so.288